Bull City Learning, Inc.
Ka’idojin Aiki
Sabuntawar Karshe: Maris, 23, 2020
Wadannan Ka’idojin Aiki suna kunshe da ka’idoji na yarjejeniya da aka yi tsakanin kai/ke, da kanka ko kuma a maimakon wani ("kai", "mai amfani", ko kuma "naka") da Bull City Learning, Inc., tare da abokan hulda da Kamfanin ("Bull City Learning", "mu", "mu", or "namu"), wanda ya danganci shiga da kuma amfani da yanar giza-gizanmu, da kuma kowane kafofin watsa labarai, tashoshin watsa labarai, gidan yanar gizo,ko kuma manhajar wayar hannu mai alaka da shi, mai nasaba ko kuma sabanin hakan wanda aka hada akai (tare, da "Shafi"). Ka/kin yarda da cewa idan ka bude wannan Shafi, ka karanta, ka fahimci, kuma ka yarda da duk wasu kaidojin amfanida aka saka don Ka’idojin Aiki. IDAN BAKI/KA YARDA DA DUKKAN WADANNAN KAIDOJIN AMFANIN BA, TOH AN HARAMTA MAKA/KI AMFANI DA WANNAN SHAFI KUMA DOLE ZAKA/KI DAKATA DA AMFANI DA SHAFI DA GAGGAWA.
Karin sharruda da dokoki ko kuma takardu da mai yiwuwa ne a sanya su a kan Shafin daga wani lokaci zuwa wani lokaci an hada su a bayyane a cikin nassoshin. Muna kiyaye da damar, cikin sirri, mu yi canje-canje ko kuma gyara wadannan kaidojin Aiki a ko yaushe kuma domin ko wane dalili. Zamu sanar da kai/ke dangane da duk wani canji ta hanyar sabuntawa "sabuntawar karshe" ranar wadannan Ka’idojin Aiki, da kuma janye duk wata dama ta karbar takamaiman sanarwa ta kowane canji. Ya rataya a wuyanka ka dinga bitar wadannan Ka’idojin Aiki daga lokaci zuwa lokaci domin ka samu masaniya a kan duk wata sabuntawa. In har ka ci gaba da amfani da wannan Shafi bayan ranar da aka dora bitar Ka’idojin Ayyuka za a dauka kana sane kuma ka yarda da duk wani bitar canje-canje na Ka’idojin Ayyuka da aka yi.
Bayanan da aka bayar a wannan Shafi ba anyi su ne domin wani mahaluki ko kuma wata kungiya su yada ko kuma suyi amfani da su ba a wata Kasa ko hurumi a inda yadawa ko kuma amfani da wadannan bayanai zai saba wa sharia da kuma kaidoji da zasu iya saka mu nemi bukatar rejista a cikin wannan hurumi ko kasa. Haka kuma, wadannan mutanen da suka zabi su bude Shafin daga wasu wurare, suna yin hakanne da himmarsu kuma sun yarda da sharruda na gida ya doru a kan su, idan kuma har sharrudan gidan za a iya zartar da su.
Wannan Shafi an yi shi ne domin masu amfani da shi wanda basu gaza shekaru 18. Ba a yarda mutane da suke kasa da shekara 18 su yi amafani ko kuma rajista a kan wannan Shafin ba.
MANUFAR TSARE SIRRI
Bull City Learning suna daraja siirin masu amfani da Ayyuka nasu. Ka/Ki koma zuwa Manufar tsare Sirri na Bull City Learning wanda zasu yi bayani a kan yadda za a karbi, amfani da, da kuma bayyana bayanai da ya Shafi sirrin ka/ki. Yin amfani da wannan Shafi yana nufin, ka yarda da Manufar tsare Sirri mu, wadanda aka hada su cikin wadannan Ka’idojin Aiki. Ana shawartar ka/ki da ka san cewa Shafi an shirya shi ne a Kasar Amurka. Idan ka bude Shafin daga kasashen Turayyar Turai, Asiya, ko wani yanki duniya wanda sharrudansu ke bukatar gudanar da tarin bayanan siiri, amfani da, ko kuma bayyanarwa da ta bambanta da sharrudan United States masu yiwuwa, toh ta hanyar cigaba da amfani da wannan Shafi, kana/kina tura bayananka ne zuwa United States, kuma ka yarda a tura bayanaka da kuma tsara su zuwa united states.
Bugu da kari, bama yarda da, bukatar, ko kuma neman bayanai daga kananun yara ko kuma cikin sani mu tallatar da ayyukan mu ma yara. Saboda haka, daidai da U. S. Children’s Online Privacy Protection Act (kamar yadda aka gyara), idan muka samu masaniya cewa wani wanda yake kasa da shekara 13 ya bamu bayanan sirri ba tare da tabbataccen yardar iyaye ba, zamu goge wannan bayanai daga kan wannan Shafi da gaggawa.
GAME DA AIKI
Abinda ke ciki, manhaja, samfuri, da/ko kuma ayyuka da aka samar a kan Shafin ("Ayyuka") anyisu ne domin bada damar bude rubutattun, bidiyo, da kuma wasu bayanai da suka Shafi batutuwa da suka hada da rigakafi, kula da lafiyar uwa, da kuma kiwon lafiya na matakin farko.
RAJISTA; DOKOKI DON GUDANARWAR MAI AMFANI; AMFANIN AIKI
Za a iya bukatar ka yi rejista da Shafin. Ka yarda zaka boye kalmar sirrin ka kuma duk hakkin amfani da asusu da kuma Kalmar sirrinka ya doru a akan wuyanka. Mun kiyaye damar cire, rikewa, ko kuma chanja sunan mai amfani da ya zaba idan muka tantance, cikin sirii, cewa sunan mai amfanin bai dace ba, na batsa ne, ko kuma ba a yarda da shi ba. Ka/kin yarda zaka/ki sanar da mu nan take game da amfani da Kalmar sirrin ka da/ko kuma asusunka da aki ba tare da izini ba. Duk wani hakkin rashi ko kuma baci da ya faru ta hanyar amfani da sunan memba, Kalmar sirrinka da/ko kuma asusunka ba tare da izini ba bai rataya a kan Bull City Learning ba.
[IKON YIN AYYUKA]
Yanar gizo mai bada bayani na BLC Institute for Learning in Global Health, mafitar koyo mai badawa domin batutuwa kan rigakafi, kula da lafiyar uwa, da kuma kiwon lafiya na matakin farko. Daga wannan shafi, masu amfani zasu iya bude mafitar koyo daban daban wanda ya hada da rukunin samfuran Immunization Academy: IA Watch, IA Learn, IA Score, da IA Manage.
Dandalin bidiyo mai daukeda fiyeda da 100 na gajerun bidiyon koyon rigakafi da turanci, Swahili, da Faransanci. Masu amfani zasu iya samun kudi domin koyon cimma nasara, gina jerin wakoki,da kuma saukar da bidiyo domin amfani ba tare da hawa yanar gizo ba. masu amfani zasu iya bude bidiyo cikin sauki ba tare da hawa yanar gizo ba a kan wayar hannu ta hanyar amfani da manhajar IA Watch Andoid. masu amfani wadanda suka yi rajista zasu iya duba aiki da kuma nasarorin sauran masu amfani wadanda suka yi rejista hade da bidiyon da suka kalla, bidiyon da suka burge su, da kuma karin girman da suka samu.
Na kyauta koyo ta yanar gizo koyo dandalin kwararrun masu rigakafi, wadda zata basu damar koyon batutuwa kamar sarkar sanyi, kula da bayanai, da kuma bada rigakafi.
Kayan aiki na gwaji domin kwararrun masu rigakafi, wanda zai basu damar gano fasaha da kuma gibin ilimi a kan gundumar, yanki, ko kuma matakin kasa.
Dandamalin koyon nazari domin masu gudanarwar rigakafi, wanda zai basu damar lura da aikin mutane da kuma kungiyoyi, sanya hanyoyi, da kuma samun gani ta hanyar rahotannin bayanai.
KAIDOJIN BIYA
Za a iya bukatar ka sayi ko kuma ka biya wasu kidi domin samun damar bude abinda ke ciki. Ka/kin yarda zaka/ki bayarda cikakkun bayanai domin siyayya da asusu, na yanzu kuma wanda suke daidai domin siyayyar da aka yi ta Shafin. Kuma ka/kin yarda zaka bada sabon bayanai nan take akan asusunka da kuma bayanan biya, hade da adreshin imel, hanyar da zaka/ki bi domin biya, da kuma ranar da katin biya zai dena aiki, domin mu samu karasa ma’amalar ka da kuma tuntubarka idan bukata ta samu. Zamu iya baka lissafi ta hanyar asusun lissafi na kan layi domin siyayyar da aka yi ta Shafin. Za a kara harajin saye da sayarwa akan kudin da zaka biya na siyayya kamar yanda zamu bukata. Zamu iya chanja kudin sayan kaya a ko wane lokaci. Duk wani biya zai kasance da dalar Amurka ta hanyar(i) amintaccen katin kudin wanda Bull City Learning zata yarda da shi, ko kuma (ii) duk wata zababbiyar hanyar biya wadda Bull City zata iya yarda da ita.
Ka/kin yarda zaka biya duk wani caji ko kudade akan kudin da aka sakawa abinda aka saya a lokacin, kuma ka bamu izinin canja mai biyan kudin da ka zaba domin wasu adadi a kan yin siyayyarka. Idan abinda ka saya ya samu maimaicin canje-canje, toh ka yarda da cajin mu na hanyar biyanka a kan maimaicin dalili batare da bukatar yardar ka ta farko ba a kan kowanne maimaicin caji, har sai ka sanar da mu game da soke mu’amalar taka. Kuma, ka fahimta da kuma yarda da cewa muna bada lissafin da kuma karbar abinda ke cikin abinda ka saya daga wajenmu a kan Shafi, kuma cewa bama cikin wata yarjejeniya tsakaninka da wani mai amfani a kan Shafin ba, kuma alhakinka bai rataya a kan mu ba dangane da wani abu da wani mai amfani ke bin ka.
Mun kiyaye damar gyara duk wani kuskure ko kuma kuskure wajen saka kudi, ko da mun bukaci ko kuma mun riga mun karbi biya. Kuma mun kiyaye damar kin duk wata oda da aka yi ta Shafin.
SOKEWA, JAYAYYA, DA CAJIN KUDI
Duk siyayyar da aka yi ba ta maida kudi bace sai dai idan Bull City Learning ta zabi ta mayarda kudin, wanda Bull City Learning zata tantance cikin sirri a kan dalilin harka zuwa wata harkar. Baka da damar dawowa da kudi ko kuma mayar da kudi domin siyayyar da aka yi a kan Shafin ko ta Ayyuka. Zaka iya soke biyan kudinka a kowane lokaci ta hanyar tuntubar mu ta amfani da TUNTUBE MU adreshin da aka bayar a kasa. Ka yarda zaka yi amfani dakasuwanci mai kwakkwaran dalili wajen kokarin aiki tare da mu da ya Shafi duk wani rashin jituwa da ya Shafi siyyar da aka yi a kan Shafin. Sokewarka/ki zata yi tasiri ne a karshen lokacin da aka biya na yanzu.
HANE-HANEN MAI AMFANI
Yin amfani da wannan Shafi yana nuna cewa, kana wakiltar da kuma bada garanti cewa: (1) duk wasu bayanai na rajista da ka bayar zasu kasance gaskiya ne, daidai ne, na yanzu ne, kuma cikakku ne; (2) zaka kula da wannan cikakken bayanai kuma nan take ka kawo Karin sabon bayani idan ya samu a yayin da aka bukata; (3) kana da iko bisa doka kuma ka yarda ka bi wadannan Ka’idojin Aiki; (4) kai ba karamin yaro bane daga hurumin da kake zaune; (5) baza ka bude Shafin ta hanyar abu mai sarrafa kansa ko wanda ba mutum ba, koda ta hanyar robot, rubutu ko abinda ba haka ba; (6) baza ka yi amfani da duk wata hanyar da ba bisa doka ba ko don dalilin da ba tare da izini ba; (7) yin amfaninka da wannan Shafi bazai saba wa wata doka ko kuma tsari ba; kuma (8)kana da amintattun lasisi da kuma takardun sheda wanda suka bayyana cewa naka ne a kan Shafin (idan zai yiyu).
Idan ka bada duk bayanin da ba gaskia bane, ba daidai ba, bana yanzu ba, ko kuma ba cikakke ba, mun kiyaye damar dakatar da ko kuma goge asusunka kuma mu hana ka kowane amfani da Shafi a yanzu ko kuma nan gaba(ko kuma wani sashi daga gare shi).
Ba tare da iyakance abin da aka ambata ba, idan kai (kana wakiltar, ko kuma kana nufin wakiltar) wani rukuni, ta hanyar amfani da Shafin da /ko kuma Ayyuka da kake wakilta kuma ka bada garanti cewa zartarwa, isarwa, da kuma isar da aiki karkashin wadannan Ka’idojin Aiki, da kuma yin amfani da mu’amalar da aka samar daga nan, an bada izinin da ya kamata daga ayyukan da suka zama dole na wannan rukuni da kuma wannan mutum (mutane) da suke amfani da Shafin da/ko kuma Ayyuka a maimakon su yana da cikakkiyar dammar daure wannan rukunin.
Dammar da aka baka domin yin amfani da Ayyuka an gina su ne kan kaidojin amfani da kuma sharrudan gudanarwa. Musamman, ka yarda baza ka/ki, a cikin kowane hali:
BAYANAI DA KE AKWAI TSAKANKANIN MASU AMFANI; TURA SAKONNI TSAKANIN MASU AMFANI
Yin amfani da wannan Shafi zai iya hadawa da rajistar asusu tare da Shafin da kuma kirkirar bayanin mutum wanda zaka iya dora wasu bayanan mutum na sirri, hadeda hoto, suna, wajen zama(kasa),kwararren sana’a, yaren da ka fi so, da kuma asusun ayyuka (wasu bidiyo ka kalla, bidiyon da ka ajiye a kan jerin kallo, bidios din da suka "burge" ka, lambar yabon da ka samu, da kuma bidiyon da ka ka tura ma wasu. Asali, wannan bayani an samar dashi ga wadanda sukayi rajista don sugani. Duk da haka, kana da zabin ka mayar da wasu daga cikin wannan bayanai naka kai kada sabida haka wasu masu amfani masu rajista baza su iya ganinsu ba. Zaka iya ganin bayanan da za a iya gani na sauran masu amfanin. Masu amfani da suka yi rajistar asusun su ne kawai zasu iya ganin bayanan martaba na mutum; ba a bada damar gani wa mutane da ziyara kawai suka kawo wa Shafin ba ba tare da kirkirar asusu ba.
Amfanin da zakayi da Shafi zaisa kuyi magana tsakanin ka da sauran masu amfani da Shafi ta hanyar tattaunawa a dandalin sakuna ko wata hanyar magana ta na’ura. Yawan sakunan da zaka dinga samu akai-akai, ko kuma rashin karbar sakon gabaki daya, zai alaka ne kalar ayyunkan da kake Ayyuka dashi da kuma yadda kake mu’amala da sauran masu amfani da Shafi.
Duk wata sadarwa tsakaninka da sauran masu amfanin dole ta bi ka’idojin amfani da aka samar a sama da kuma kin abinda ke ciki na kan layi daya biyo baya. Ka yarda zaka biya mu dukkan ikirari, kudade, da kuma diyya wanda ya Shafi kasa bin kaidojin mu na nan. Idan ka zabi ka fadawa sauran masu amfani bayanan sirri ta hanyar sadarwa a kan Shafin, ka yi hakanne da sanin hadarin yin hakan, kuma baza mu baka tabbacin cewa wannan bayanan sirrin za ka a basu kariya ba. Bugu da kari, idan sadarwarka da sauran masu amfani ya jawo wasu hanyar sadarwa na waje da basu da alaka da wannan Shafi, ka wakilci kuma ka yarda cewa wannan sadarwa bata daga cikin kariyar Ka’idojin Ayyuka ko kuma Manufar tsare Sirrin ka. Kana yin wannan sadarwa a sane da hadarin da ke cikinta.
KIN ABINDA KE CIKI NA KAN LAYI
Ra’ayi, rawaitowa, shawara, kiyastawa, sanarwa, tayi, da kuma sauran bayanai ko kuma abinda ke ciki da aka samar ta hanyar Aiki, amma ba kai tsaye daga Bull City Learning ba ("mai amfani da abinda ke ciki"), sune na marubutan su, kuma ba lallai a dogara dasu ba. Su wadannan marubuta abinda ke ciki ya rataya a kansu. Bull City Learning bata bada tabbacin daidaiton, cikar, ko kuma amfanin wani bayanai a kan Shafin ba, kuma Bull City Learning bata dauko ko kuma bada goyon baya ba, kuma hakki bai rataya akan Bull City Learning ba domin daidaiton ko kuma amincin ko wani abun ciki da amfani. Babu alhakinka a kan Bull City Learning game da duk wani abin da ke ciki na amfani da ka ko kuma abokan aiki na waje kuka dora ko kuma tura a kan Aiki. Ko da a karkashin wane yanayi ne, Bull City Learning baza ta dauki alhakin wani rashi ko kuma lalacewa da tayi sanadiyya daga dogaro a kan bayanai ko kuma abin da ke ciki da aka dora a kan Shafin ba, ko kuma aka watsa zuwa ga masu amfani.
Duk da cewa Bull City Learning tana da zummar tilasta wadannan Ka’idojin Aiki, zaka iya ganin abinda ke ciki na amfani wanda ba dai-dai ba ko kuma wanda baka yarda dasu ba. Bull City Learning ta kiyaye damar, amma bata da takalifi, na duba kayan aiki da aka dora a kan sashen ayyuka na jama’a ko ta saka iyaka ko kuma hana mai aiki bude Shafin ko kuma ta dau matakin daya kamata idan mai amfani ya keta wadannan Ka’idojin Aiki ko kuma yayi wani aiki da ya keta damar wani mutum ko kuma rukuni ko kuma wanda muka ga ya ketare doka, mai jawo bacin rai, cin mutunci, cutarwa ko kuma mai keta ga masu amfani. Sako na kai tsaye ko imel da aka tura tsakanin kai da sauran al’umma da sauran jama’a baza su samu damar bude su ba ko kuma babbar al’umar Bull City Learning zamu duba su da kanmu a matsayin kebabben lamari har zuwa inda doka ta bukata. Bull City Learning zata kiyaye damar cire duk wani kayan aiki da a ganinta ya ketare doka, ko kuma ake zargin ya ketare doka, shari’a, ko kuma yarjejeniya ko kuma wanda zai jawo bacin rai, ko kuma wanda ya keta damar, cutar da, ko kuma, ko kuma ya bada barazana galafiyar masu amfani ko kuma wanu. Amfani ba tare da izini ba zai bada sakamakon yin laifi da/ko kuma shigar da kara karkashin dokar gomnatin tarayya, jiha ko kuma na karamar hukuma. Idan ka lura da amfani da Ayyukan mu ko kuma Shafin mu ta hanyar da ba daidai ba, a TUNTUBE MU a kan adreshin da muka samar a nan kasa.
HANYOYIN HADI ZUWA WASU SHAFUKA DA/KO KUMA KAYAN AIKI
A matsayin sashin Aiki, Bull City Learning zata iya samar maka da hanyoyi da suka dace zuwa Shafi (shafukan) abokan aiki na waje ("shafukan abokan aiki na waje") haka kuma abinda ke ciki ko kuma abubuwa da daman na abokan aiki na waje ne ko kuma dama sun samo asali ne daga abokan aiki na waje ("manhajar abokan aiki na waje, manhaja ko kuma abin da ke ciki"). Bull City Learning bata da damar sarrafa shafuka da kuma manhajar abokan aiki na waje, manhaja ko kuma abinda ke ciki ko kuma gabatarwa, kayan aiki, bayanai, kayayyaki ko kuma ayyuka da za a iya samunsu a kan shafuka ko kuma manhajar abokan aiki na waje, manhajar ko kuma abinda ke ciki.
Bull City Learning bata binciken, duba, ko kuma duba daidaiton, dacewar, da kuma cikar wadannan shafuka da kuma manhaja, manhaja da abinda ke ciki, kuma Bull City Learning bata dau alhakin bude wani Shafi ko manhaja ta abokan aiki na waje ba, manhaja, ko abinda ke ciki da aka bude su ta wannan Shafi da zai samu a kan ko kuma ta hanyar kafawa daga Shafin, wanda ya hada da abinda ke ciki, daidaiton sa, mai jawo bacin rai ne, ra’ayi, dogaron sa, bayanin tsare sirri ko wasu manufofin da suke cikin shafuka da manhajar abokan aiki na waje, manhaja ko kuma abinda ke ciki. Tare da, hadawa zuwa ko kuma bada izinin amfani da ko kuma kafa duk wani Shafi ko manhajar abokan aiki na waje, mahaja ko kuma abinda ke ciki, ba yana nufin amincewar ko kuma bada goyon bayan Bull City Learning bane. Idan ka yanke shawarar barin Shafin da kuma bude shafunkan abokan aiki na waje ko kuma ka yi amfani da ko kuma kafa wani manhajar abokan aiki, manhaja ko kuma abinda ke ciki, kan yin hakan ne da sanin hadarin da ke ciki kuma ka sani cewa baya karkashin ka’idojin amfanin mu. Ya kamata ka yi bitar ka’idojin manufofin, wanda ya hada da sirri da kuma tarin bayanan ayyuka, da duk wani Shafi da ka kewaya daga Shafin ko kuma wanda yake da alaka da wasu manhajoji da ka yi amfani dasu ko kuma ka kafa daga Shafin.
KORAFIN HAKKIN MALLAKA DA KUMA WAKILIN HAKKIN MALLAKA
(a) Kawowa karshen asusun maimaita keta. Bull City Learning tana girmama damar dukiyar mai hankali na wasu da kuma bukatar masu amfani suma su kiyaye wannan dama. Bin dokar hakkin mallaka ta United States ta 17 U.SC. 512(i)(kamar yadda aka gyara), Bull City Learning ta dauki kuma ta aiwatar da wata manufa da zata bada damar kawo karshen a cikin halin day a kamata na masu amfani da Shafin da/ko kuma Ayyuka wanda suke masunmaimaita keta. Bull City Learning zata iya kawo karshen samun damar budewa ta mahalarta ko kuma masu amfani wanda aka samesu da maimaicin samarda ko kuma dora abin da ke ciki na abokan aiki na waje mai kariya batare da dama da kuma izini daya dace ba.
(b) DMCA Sanarwar Saukarwa. Idan kai ka mallaki hakkin mallaka ko kuma kai wakili ne kuma ka yarda, cikin kyakkyawan imani, cewa duk wani kayan aiki da aka samar a kan Shafi ya ketara hakkin mallakar ka, zaka iya bada sanarwa ta bi zuwa ga Digital Millenium Copyright Act (a yadda aka gyara, a duba 17 U.S.C 512) ("DMCA") ta hanyar tura bayanai masu zuwa a rubuce zuwa ga wakilin hakkin mallaka na Bull City Learning a: 102 City Hall Plaza, Suite 200, Durham, NC 27701.
(c) Sanarwar ta kin yarda. Idan har kana tunanin cewa abin ciki na amfaninka wanda aka cire daga kan Shafin ban a kete bane, ko kuma kana da izini daga wajen mai hakkin mallaka, wakilin mai hakkin mallaka, ko kuma mai bin shari’ar, domin a dora ko kuma a yi amfani da abinda ke ciki na abinda ke ciki na mai amfani, zaka iya tura sanarwa ta rashin yarda wadda zata kunshi bayanai da zasu biyo baya zuwa ga wakilin hakkin mallakar mu ta hanyar amfani da bayanan tuntuba da aka saka a gaba.
Idan wakilin hakkin mallaka na Bull City Learning ya samu sanarwar kin yardar mu, Bull City Learning zata iya tura kopin sanarwar zuwa ka asalin mai korafin don ta sanar da shi cewa zata iya mayar da abinda ke ciki da aka cire a cikin ranakun aiki 10. Sai dai idan mai hakkin mallaka ya dau matakin shigar da kara a kotu a kan mai samar da binda ke ciki, mamba ko kuma mai amfani, abinda ke ciki din da aka cire (cikin sirrin Bull City Learning) za a iya mayar das hi kan Shafin a cikin kwanakin aiki 10 zuwa 14 ko fiye da haka bayan an samu sanarwar kin yardarm.
BADA LASISI
Dora kowane abinda ke ciki mai amfani ta hanyar Aiki, yana nufin ka bada izini, kuma kana wakilci da bada garanti din cewa kana da damar bada izini, ‘yanci zuwa ga Bull City Learning, iya bada lasisi, za’a iya mayarwa zuwa wani waje, na dindindin,babu warwarewa, babu kebewa, lasisin amfani duk duniya, sake yin wani, gyarawa,wallafawa, jero bayanai dangane da, gyarawa a rubuce, fassarwa, rarrabawa, yi a fili, nunawa a fili, da kuma yin wanda ya samo asali daga ayyukan wadannan abibda ke ciki mai amfani da kuma sunanka, muryarka, da/ko kuma kama da ke kunshe cikin abinda ke ciki na amfaninka, in zaai yiwu, gaba daya ko kuma wani sashe, game da duk wani tararre da kuma boyayyen bayanai daya samo asali daga abinda ke ciki mai amfani, kuma a kowane kamala, ta kafofin watsa labarai ko kuma fasaha, koda sananne a yanzu ko kuma daga baya aka habbaka shi, domin amfani dashi dangane da Aiki.
DUKIYA TA MAI HANKALI
Sai dai inda aka nuna, Shafi da Ayyuka dukiyarmu ne na cancanta da kuma duk lambar tushe, bayanai, aiki, manhaja, zanen yanar gizo, sauti, bidiyo, rubutu, hotuna, da kuma zane a kan Shafi (a hade, da "abinda ke ciki") da kuma alamar kasuwanci, alamomin aiki, da kuma tamburan da suke kunshe ciki ("alamomin") mallakarmu ne ko kuma an bamu lasisinsu, kuma hakkin mallaka ya kare su da kuma dokar alamar kasuwanci da kuma sauran damar mallakar dukiya da kuma dokar rashin adalci ta United States, hurumin kasashen waje, da kuma taron duniya. Abinda ke cikin da kuma alamomi da aka samar akan Shafi da Ayyuka "kamar yadda yake" domin saninka ko kuma amfaninka na sirri ne kawai. Sai dai a inda Ka’idojin Aiki suka samar, ba a bada damar a kwapi wani bari daga Shafin da/ ko kuma Ayyuka da kuma abinda yake ciki da kuma alamomi da suke ciki ba, sake yi, Tarawa, sake walafawa, dorawa, sakawa, nunawa a fili, rikidawa, fassarawa, watsawa, rarrabawa, sayarwa, lasisi, ko kuma abinda ya sabawa amfani da shi domin dalilan kasuwanci kowane iri, ba tareda bayyanawarmu ta izini a rubuce kafin komai ba. Bamu bada garanti din cewa abinda ke ciki zai yi aiki ba tare da katsewa ba ko kuma ba tare da kuskure ba ko kuma kowane kuskure za a gyara shi ba. Bugu da kari, bamu bada garanti din cewa abinda ke cikin ko kuma duk wani kayan aiki, tsari ko kuma hanyar sadarwa wadda abinda ke cikin aka yi amfani das hi zai kasance babu wani hadarin kutsawa ko kuma kawo hari.
In har ka/kin kai a baka damar amfani da Shafin da kuma Ayyuka, an baka izini mai iyaka na lasisin budewa da kuma amfani da Shafin da kuma Ayyuka da kuma saukewa ko kuma bugawa a kan takarda kwafi daya na kowane sashin abin da ke ciki wanda ka ka samu damar bude shit a hanya madaidaiciya domin amfanin sirrinka, kuma ba don kasuwanci ba. Mun kiyaye damar baka izini ciki ko zuwa Shafin, Ayyuka, abinda ke ciki da kuma alamomi. Zamu kasance a duk lokuta rike da duk wata mallaka ta abinda ke ciki wanda aka sauke shit un asali ko kuma ka yi amfani da shi da kuma dukkan abinda aka sauke na daga baya na abinda ke ciki domin amfaninka. Abinda ke cikin (da kuma hakkin mallaka, da wasu dukiya ta hankali dama ta kowace irin kamala a cikin abin amfanin, game da duk wani gyararraki da akayi a can) sun kasance kuma zasu kasance mallakinmu. Mun kiyaye damar bada lasisi domin amfani da abinda ke ciki ga abokan aiki na waje.
Yin amfani da wannan Shafin da kuma Ayyuka, yana nufin ka bada izini wa Bull City Learning ta yi amfani da, sake amfani da, da kuma bada izini wa wasu damar amfani da kuma sake amfani, ba tare da an biya ka komai ba, alamun kasuwancin, sunayen kasuwancin da kuma tamburan ka a kan ko wane kafar yada labarai wadda aka sani yanzu ko kuma nan gaba. Wadannan amfani zasu kasance na yadda aka saba da kuma kasuwanci ta hanyar day a kamata domin kasuwanci, gabatarwa da kuma sauran dalilai day a kamat masu alaka da Shafin da/ko kuma Ayyuka, da kuma kasuwancin mu, da kyakyawan imanin hukuncin mu akan kowani amfani.
IMEL BAZAI IYA KASANCE WAJEN SANARWA BA
Sadarwa Aiki da akeyi ta imel da na’urar sakonni, bazai zama tangarda ba ga manya, ma’aukata, ajan ko wakilan Bull City Learning a duk wani yanayi na shari’a ko wata doka a kan Bull City Learning.
AMINCEWAN MAI AMFANI DON KARBAR SAKONNI TA HANYAR FOM DIN SHAFI
Sabida dalilan yarjejeniya, (a) ka amince da karbar sakonni kan layi daga Bull City Learning ta hanyar adireshin ka na imel da ka bayar; kuma (b) ka yarda Ka’idojin Aiki, yarjejeniya, sanarwa, tonawa, da wasu sadarwa da Bull City Learning yake bayarwa zuwa gareka ta kan layi don gamsar da abinda ake bukata wanda zaiyi daidai da kaman an rubuta a takarda. Wannan bai taba hakkokin ka da zaka iya canjawa ba. Zamu kuma iya amfani da adireshin imel dinka don turo maka wasu sakonnin, harda bayanai akan garabasoshi na musamman na Bull City Learning. Zaka iya fita daga irin wannan sakonnin na imel ta hanyar canja saitin asusun ka idan ka tuntubi ma’aikatan mu a support@BullCityLearning.
Fitan zai hanaka samun sakonni akan garabasoshi na musamman na Bull City Learning.
GYARAN KA’IDOJIN AIKI
Zamu iya gyara wadannan Ka’idojin Aiki a duk wani lokaci kuma zamu canja wadannan Ka’idojin Aiki idan ansamu wani cigaba. Hakkin ka ne ka dinga duba Shafin lokaci zuwa lokaci don ganin irin wannan canjin a yarjejeniyar. Idan ka cigaba da amfani da Shafin, ka nuna amincewan ka ga yarjejeniya da gyaran wadannan Ka’idojin Aiki. Duk da haka, zamu sanar dakai akan idan ansamu canji a ka’idojin ta hanyar sanarwa a Shafin mu na farko da/ko kuma ta hanyar tura maka sakon imel din da kabamu lokacin da kayi rajista. Sabida wannan karin dalilin, ka ajiye bayanan ka da lambar tuntubanka bisa yadda suke a yanzu. Duk wani canji ga wannan ka’idoji (banda yadda akayi bayani anan) ko hakkokin Bull City Learning bazai zama mai inganci ba ko amfani sai ansamu rubutacciyar yarjejeniya me dauke da saka hannu ma’aikacin Bull City Learning a zahiri. Babu wani gyara ko abu na wannan yarjejeniya na Bull City Learning ta hanyar sakonnin imel zai kasance mai kyau.
KULA DA SHAFIN
Bull City Learning nada damar, amma ba dole ba, yin: (1) lura da Shafin don duba karya dokar Ka’idojin Aiki; (2) daukan matakin shari’a akan duk wanda ya karya dokar ta Ka’idojin Aiki a bainar mu, ta hanyar kai kararsa zuwa ga jami’an tsaro; (3) a wajen mu ba tareda wani ka’ida ba, mu ki, hana shiga, dakatar da, ko (rufe duka wani taimako) ko wani gefen; (4) a wajen mu ba tareda wani ka’ida ba, sanarwa, mu cire duka wani failika da rubutu wadanda sukayi wa na’urorin mu nauyi ko sukafi karfinsu; kuma (5) ko kuma lura da Shafin a hanya da aka tsara don kula da hakkokin mu da dukiya da kuma lura da tabbatar da ayyukan Shafin.
KA’IDA DA YANKEWA
Wannan Ka’idojin Aiki zai kasance yana aiki sosai duk lokacin da kake amfani da Shafin, kuma zai cigaba har sai kayi da sauri (i) ka sanar da mu a rubuce cewa kanason fita, (ii) ka kasa bada hadin kai ga yarjejeniyar wannan Ka’idojin Aiki, ko (iii) mun yanke ko rufe asusun ka. BA TAREDA RAGE WANI KA’IDAN WADANNAN KA’IDOJIN AIKI, MUNADA IKON YIN, A WAJENMU BA TAREDA SANARWA BA, HANA DAMAR AMFANI DA SHAFIN (HARDA TARE WASU ADIRESHIN IP), GA KO WAYE BISA DALILI KO BABU DALILI, HARDA BABU KA’IDA NA CIN AMANA, KO KUMA KARYA ALKAWARIN A CIKIN WADANNAN KA’IDOJIN AIKI KO KUMA WANI DOKOKI. ZAMU IYA YANKE AMFANI KO GUDUNMAWAR KA A SHAFIN KO GOGE ASUSUN KA DA WANI RUBUTU KO BAYANI DA KASAKA A KOWANNE LOKACI BATARE DA SANARWA KO KASHEDI BA.
Idan muka kulle ko dakatar da asusun ka sabida wani dalili, za’a yanke lasisin da aka baka na Ka’idojin Aiki kuma bazaka sake amfani da Shafi da/ko Ayyukan mu ba. An haramta maka yin rajista da bude sabon asusu idan kayi amfani da sunan bogi ko na aro, ko sunan wani awaje, ko da kanayin hakan ne akan wakilci. Karin bayani akan yankewa ko dakatar da asusun ka, munada damar daukan matakin shari’a, harda bin duka hanyoyin gurfanar da kai a gaban shari’a.
GYARA DA DAKATARWA
Munada damar canza, gyara ko cire rubutu daga Shafin mu a kowanne lokaci ko wani dalili awajen mu batare da sanarwa ba. Duk da haka, bamuda niyyan sabunta wani bayani a Shafin mu. Kuma munada damar canja ko daina komai ko wani fannin Shafin a kowanne lokaci batare da sanarwa ba. Bazamu dauki laifi gare ka ko abokan hudda na waje ba idan mukayi gyara, canjin farashi, dakatarwa ko daina ayyukan Shafin nan.
Bazamu baka garanti cewa wannan Shafin zai kasance a koda yaushe. Zamu iya haduwa da tangardan na’ura, manhaja ko wasu matsalolin ko kuma bukatan yin gyara ga shafukan, wanda zai iya kawo tsayawa, da sauran matsala. Munada daman canja, gyara, tsayarda ko kuma canja Shafin a ko wanne lokaci ko wani dalili batare da sanarwa ba. Kayarda cewa bazamu dauki alhakin ko wani iri idan ka hadu da rashi, lalacewa ko rashin jindadi a dalilin kasa shiga Shafin ko amfani dashi lokacin da yake fuskantar matsala ko idan muka rufe Shafin. Bawani abu acikin Ka’idojin Aiki da zai samu dole mu lura da taimaka wa Shafin ko kawo wani gyara, ko labarai cikin sa.
GYARARRAKI
Za’a iya samun bayanai acikin Shafin nan dauke da kuskuren rubutu, kura-kurai, ko ragewar bayani, harda kwatance, farashi, samuwa, da sauran bayanai. Munada damar gyaran duka kuskuren, kura-kuren, ko ragewar bayani da kuma canja ko sabunta bayani a Shafin da/ko Ayyuka a kowanne lokaci batare da sanarwa ba.
GARANTIN RASHIN ALHAKI
SHAFIN DA AYYUKAN ANA GABATAR DASU NE "AKAN," BATARE DA GARANTI NA KO WANE IRI. BA TARE DA SAKA IYAKA BA, Bull City Learning BATA YARDA DA DUKKAN WANI IKRARI, DUKKAN GARANTI, KO A BAYYANE, NUNI KO KUMA DOKA, DANGANE DA AIKI GAME DA BA TARE DA IYAKA BA DUK WANI GARANTI NA CINIKI, DACEWA DA DALILI NA MUSAMMAN, SUNA, TSARO, DAIDAITO DA KUMA RASHIN KETA. BA TARE DA SAKA IYAKA BA, Bull City Learning BATA BADA WANI GARANTI KO KUMA WAKILCIN SAMUN BUDE KO KUMA AIKIN DA BA ZAI KATSE BA KO KUMA MARA KUSKURE. HADARIN RASHI TA DALILIN SAUKARWA DA/KO KUMA YIN AMFANI DA FAYIL, BAYANAI, ABINDA KE CIKI KO KUMA WASU KAYAN AIKI DA AKA SAMO DAGA KAN AIKI SUN RATAYU A KANKA. WASU IYAKAR HURUMI KO KUMA KAR A BADA IZININ IKIRARI NA GARANTI, SABODA HAKA WANNAN BA LALLAI YA SHAFE KA BA.
IYAKAR DIYYA; SAKEWA
HAR ZUWA INDA DOKA TA BADA IZINI, BABU CIKIN KO WANE YANAYI DA ZAI SA Bull City Learning, MASU HULDA DA ITA, DARAKTOCI, KO MA AIKATA, KO KUMA MASU LASISINTA KO KUMA ABOKAN AIKINTA, HAKKIN KOWANE RASHI NA RIBA DA KA SAMU ZAI RATAYA A KANSU, AMFANI, KO KUMA BAYANAI, KO KUMA DOMIN WANI ABINDA YA FARU, A KAIKAICE, NA MUSAMMAN, SAKAMAKON KO KUMA MISALAN DIYYA, KO YAYA SUKA TASO, DA SUKA FARU A SABILIN (A) AMFANIN, BAYYANA WA, KO KUMA NUNA ABINDA KE CIKI NA AMFANI NAKA; (B) AMFANINKA NA KASA AMFANI DA AIKI; (C) BAKI DAYAN AYYUKA KO KUMA MANHAJAR KO KUMA TSARUKA DA SUKE IYA SAMUWA NA AIKI; KO KUMA (D) DUK WANI MU’AMALA DA Bull City Learning KO KUMA WANI MAI AMFANI NA AIKI, KO DA A DALILIN GARANTI, LAMBA, HORO, (TARE DA SAKACI) KO KUMA KOWANE KA’IDAR DOKA, KUMA KO HAKA KO BA HAK BA AN SANAR DA Bull City Learning A KAN YIWUWAR DIYYA, KUMA KO MAFITA DA AKA TURA A NAN TA KASA SAMUWA DOMIN MUHIMMIN DALILANSA. WAS HURUMAN KUNA SAKA IYAKA KO KUMA BASA BADA IZININ RASHIN YARDA NA ALHAKI, SABODA HAKA WANNAN BA LALLAI YA SHAFE KA BA.
Idan ka samu rashin jituwa da da ko kuma wasu daga cikin masu amfanin ka sake mu(da ofisoshinmu, daraktocinmu, wakilanmu, da masu wakilta na biyu, hadin gwiwowi da kuma ma’aikatanmu) daga wasu ikirari, bukatu, da kuma diyya (na ainahi ko kuma na sakamako) na kowane irin kama, sananniya ko ba sananniya ba, wanda ya taso daga duk wata hanya da ta Shafi rashin jituwar. Idan kana zaune a garin California ne, ga jingina da lambar jama’a ta garin Carlifornia § 1542, wanda ya ce: "Saki na baki daya bai kai har ikirarin wanda mai biyan bashi bai sani ba ko kuma bai yi zargin samuwarsa ba domin amfaninsa ba a yayin zartar da sakewar, wanda idan har ha sani dole ya Shafi sulhunsa da mai binsa bashi."
BIYAN DIYYA
Ka yarda ka kare, biyan diyya, ka dauke mu da cibiyoyin mu, abokan hudda, da sauran duka ma’aikatan mu, abokan aiki, daractoci, da wakilan mabuda laifi a rashi, dameji, asara, ko bukata harda kudin biyan mai shari’a da wanda wani abokin hudda na waje ya bukata sabida: (1) abinda ka rubuta; (2) amfani da Shafin da/ko Ayyuka; (3) karya dokar Ka’idojin Aiki; (4) duk wani karya doka akan wakilci da garanti da aka saka a Ka’idojin Aiki; (5) karya dokar abokin hudda na waje harda kayansu; ko (6) duk wani abu mara kyau da kayi ga wani mai amfani da Shafin wanda kuka hadu a Shafin. Munada damar, a gaban ka, mubi duk wani hanyar kare kanmu da duk wani harka da yake bukatan diyya awajen mu, kuma ka yarda ka bada hadin kai, a matsayin ka, da kariyan mu. Zamuyi kokari mu sanar dakai hakan, mataki, ko wani dalili da zai kawo biyan diyyan domin kasani. Ka yard aka mayar mana da kudi shari’a da mukayi idan muka bukaci ko wani asara da mukayi, ko ta kotu ko sulhu.
Idan doka ta hanaka shiga wannan biyan diyyan, sai kayi tunani ga abinda doka yace, duk wani asara, kasha kudi, neman (harda kudin da aka biya mai shari’a, nawa yaci, da kudin shedu) sune abubuwan da suka bukaci diyyan.
BAYANAN MAI AMFANI
Zamu ajiye wasu bayanai da ka watsa zuwa Shafin sabida amfani dashi wajen gudanar da Shafin, tare da bayanai akan kadda kake amfani da Shafin. Duk da muna ajiyan bayanan akai-akai, duk wani bayanai da ka watsa ko wacce take da alaka da wani aiki da kayi a Shafi yana wuyanka. Ka yarda cewa babu laifin mu idan bayanan sun bata ko sun lalace kuma bazaka dauki wani mataki akan mu sabida bata ko lalacewar wannan bayanan.
TURA SAKO TSAKANIN MASU AMFANI DASHI
Amfanin da kakeyi da Shafin zai iya hada da Ayyukan sadarwa tsakaninka da sauran masu amfani ta hanyar sakon SMS/MMS, imel da sauran hanyoyin sadarwa da na’ura. Yawan sakunan da zaka dinga samu akai-akai, ko kuma rashin karbar sakon gabaki daya, zai alaka ne kalar Ayyunka da kake amfani dashi da kuma yadda kake mu’amala da sauran masu amfani da Shafin.
Akwai biyan kudi wajen turawa da karbar sakonni da amfani da yanar gizo, kamar yadda kamfanin salula suke karba a tsarin su, akan karin biya idan a kasar waje kake amfani dashi. Ka tuntubi kamfanin wayar salulan ka don jin farashi da bayanai. Saidai idan ansaka shiga ko anyi yarjejeniya da muka saka a ayyukan mu, bam akum bazamu cajeka kudi dabam ban a tura sakonni.
Ka tabbatar da cewa lamba (lambobi) wayar da kabayar na asusun ka ne. Zaka sanar da Bull City Learning cewa ka canja lambar ta hanyar tuntubar Bull City Learning a adireshin TUNTUBAR MU da aka bayar a kasa.
A duk lokacin da kake da bukatan daina karbar sakon tes, Bull City Learning zai baka lambobi da zaka tura STOP duk lokacin da kakeson daina karbar sakonnin. Sannan zaka ga tabbacin fita daga tsarin karbar sakonnin. Zaka iya tuntubar Bull City Learning ta adireshin TUNTUBAR MU wanda aka bayar a kasa wanda daga nan bazaka sake samun sakonnin ba.
Ka yarda da diyya ga Bull City Learning ga duka abinda suke nema, kudin da suka kashe, da tara daga ko akan kasa fadi Bull City Learning idan ka canja lambar wayanka, ga duka abinda suke nema, kudin da suka kashe, da tara daga ko bisa Telephone Consumer Protection Act (yadda aka gyara).
BAMA WAKILCI
Babu mai amfani da wannan Shafi ko Ayyuka da aka bashi dama ya dau kwantiragi, yarjejeniya, garanti ko wakilci amadadin mu ko yayi wani aikin, ko maganganu a madadin mu. Bazaka yi sojan gona ba ko kace kana wakiltar mu a matsayin ma’aikaci, abokin hudda ko na kasuwanci.
MAZAUNA CALIFORNIA DA MASU AMFANI DASHI
Idan baka gamsu da yadda muka sasanta korafinka ba, zaka iya tuntuban mai karban korafe-korafe a sashen Consumer Services of the California Department of Consumer Affairs a rubuce a Department of Consumer Affairs, Consumer Information Division, 1625 North Market Blvd., Suite N 112, Sacramento, CA 95834 kp lambar waya (800) 952-5210.
DAUKAN MATAKI DA SULHU
DUK WANI RIKICI,RASHIN JITUWA, KO NEMAN HAKKI DA YA TASO KO NASABA DA WANNAN YARJEJENIYA, HARDA ZAMBA, YANKEWA KO AKAN INGANCI, ZA’A SASANTA SU NE TA HANYAR SULHU. MAJALISAR SULHUN SUNA DA DAMAR ZARTAR DA HUKUNCI AKAN DUKA RIKICI A IYAKAR TA KO ZUWA INDA KO TILASTA AKAN GEFEN YARJEJENIYA DA ZA’AYI SULHU. GEFEN MASU RIKICIN SUN YARDA AYI SULHU BISA KAN DAI-DAYA, KUMA SUN YARDA WANNAN SULHUN DA YARJEJENIYA BAI BADA DAMA SULHUN CIKIN AJI BA KO NEMAN ABU DAGA WAJEN MAI KARA KO MEMBAN AJI KO SULHUN WAKILCI. MAJALISAR SULHUN BAZAI KARFAFA AKAN SAMA DA KARAR MUTUM DAYA BA, KUMA BAZAI YI SULHU BISA WAKILCI BA KO ACIKIN AJI. A INDA AKE GANIN SULHUN CIKIN AJI BAIDA INGANCI KO BABU TILASTAWA, TO SAURAN BANGARORIN YARJEJENIYA SULHUN ZAI CIGABA DA AIKI.
BATARE DA IYAKANCE YADDA AKE TAFIYA BA, KO WANNE BANGARE ZASU AJIYE HAKKIN SU NA NEMA AKAN DAYA BANGAREN A MATSAYIN WAKILCI KO MEMBA A KOWANNE AJI KO AIKIN WAKILI. IDAN KUMA DOKA KO KOTU TA BAMA BANGARE DAMAR YI A AJI KO KAWO MAI WAKILCI AKAN DAYAN BANGARE, TO DOLE DUKA BANGAREN ZASU YARDA DA: (I) GEFEN MASU KARA BASUDA DAMAR DAWO DA KUDIN MAI SHARI’A KO KUDIN DA AKA KASHE AWAJEN AJI KO WAKILI (IDAN BABU WANI ABU DA YAHANA DOKAR); DA (II) BISA YARJEJENIYA BANGAREN DA YAFARA SHIGA A MATSAYIN MEMBA NA AJIN BAZAI TURA KORAFI KO SHIGA SAMUN ABINDA YAFITO TA AJIN KO AIKIN WAKILI.
KA’IDOJI GABA DAYA
Idan wani bangaren wannan yarjejeniya ya kasance mara amfani, gefen da yarjejeniya zaiyi amfani za’ayi amfani dashi bisa doka. Sauran fannonin zasu kasance sun fara aiki da karfin su. Duk wani matsala daga Bull City Learning wajen tilasta yarda da wannan yarjejeniya bazai kasance wani dama akan hakkin mu na tilasta hakan. Hakkokin mu a karkashin yarjejeniya nan zai rayu akan yankewar wannan yarjejeniya.
Ka yarda cewa duk wani mataki mai kusanci ko yafito daga cikin mu’amala da Bull City Learning yazama dole afara cikin shekara daya bayan daukan matakin. Idan ba haka ba, wannan matakin yazama babu har abada.
Wadannan Ka’idojin Aiki da amfani da Shafi suna karkashin dokokin tarayya na Kasar Amurka da dokokin Jahar North Carolina, batare da duba banbancin dokokin ba.
Bull City Learning zasu iya saka ko tura wakilcin wadannan ka’idojin aiki da/ko Manufar tsare Sirri na Bull City Learning, gaba daya ko wani fanni, ga wani mutum ko wani abun a kowanne lokaci da yardar ka ko babu. Bazaka saka ko wakilta wani ka’idoji ko yin dole bisa Ka’idojin Aiki ko Manufar tsare Sirri na Bull City Learning ba tare da an baka izini ba, kuma duk wani da kasaka ko ka wakilta a banza ne.
KA/KIN YARDA CEWA KA KARANTA WA’ANNAN KA’IDOJI AIKI, KA FAHIMCI SHARRUDAN SABIS, KUMA ZAKA BI WA'ANNAN KA’IDOJI AIKI. KUMA KA/KIN YARDA DA WA'ANNAN KA’IDOJIN AIKI TARE DA MANUFOFIN TSARE SIRRI SUNA WAKILTAR CIKAKKEN BAYANI NA YARJEJENIYA DA YAKE TSAKANIN MU KUMA YAFI DUK WANI YARJEJENIYA NA BAYA A BAYYANE KO A RUBUCE, DA DUK WANI SAURAN SADARWA TSAKANIN MU BISA USULIN MAGANAN WANNAN YARJEJENIYA.
FARASHI DA KUDIN LAUYA
Idan muka nemi taimakon mai shari’a wajen karbar kudin mu ko kawo wani mataki akan ka, a bayyane ko wata hanyar, a bisa Ka’idojin Aiki, kuma shari’ar tazama nasara garemu, ko sulhu, ka yarda zaka biya kudin da muka biya na shari’a duk abinda muka kashe, ko ta sulhun ko shari’a ko daukaka kara.
TUNTUBE MU
Domin warware korafi a game da Shafin ko kuma don samun karin bayani game da amfani da Shafin, a tuntube mu a: [email protected].