Manufar tsare Sirri

Bull City Learning, Inc.

Manufar tsare Sirri

Hakkoki da tonawa na California

Bull City Learning, Inc., tare da abokan harkokin su ("Bull City Learning", "mu", "mu", ko kuma "namu") ya dau alkawarin tsananta kare bayanan sirrinka, ko naka ko kuma amadadin mukarraban ka ("kai", "mai siya", "mai amfani", ko kuma "naka").

Karin bayani akan hakkoki da aka bayyana a Manufar tsare Sirri yana aiki akan kowa, a wasu yanayin, mazauna California sun kasance sunada hakkoki bisa wasu bayanai da aka karba, amfani, da kuma rabawa bisa manufar tsare sirri.

Don wadannan dalilai, "Shafi" yana nufin shafuka, dandali, akwatunan sada zumunta, ko manhajar waya wanda za’a iya samun ayyukan koyo na Bull City a inda mai amfani zai iya ganin shafuka kuma yasamu izinin amfani da manhaja, kayayyaki, da ayyuka ("Aiki," gabaki daya "Ayyuka").

Don Allah ka samu lokaci ka karanta wannan Manufar tsare Sirri sabida sirrin ka yanada muhimmanci awajen mu. Idan kanada wata tambaya akan yadda muke karbar bayanai, amfani, karewa ko yadda muke amfani da Bayanan ka (kamar yadda mukayi bayani a kasa), ka tuntube mu ta hanyoyin sadarwar mu dake kasa.

Saidai idan an canja yadda aka ayyana a wannan Manufar tsare Sirri, sharuda da aka yi amfani dasu a Manufar tsare Sirri suna daidai da Ka’idojin Aiki. Idan kayi amfani da hajojin mu, ka amince da karba, ajiya, amfani da bayyana bayanan kanka bisa yarjejeniyar da aka sanya.

  1. BAYANAI DA MUKE KARBA, SIYARWA, DA KUMA RABAWA
  2. Muna karba da raba bayanai kamar yadda aka kwatanta a Sashi I da Sashi II na Manufar tsare Sirri. Kamar yadda yake a rukunin bayanai na Sirri na abokin ciniki na California kundin 2018:

    • Muna karbar bayanan ganewa, duka bayanan abokin ciniki, yanar gizo da sauran bayanan ayyukan shafukan yanar gizon, bayanan daidai inda yake, bayanai akan irin sana’a da wasu sauran bayani.
    • A watanni goma sha biyu da suka wuce, bamu siyar da bayanai na kowa ba.
    • A watanni goma sha biyu da suka wuce, munyi amfani da ko wacce kalar bayanai da muka karba sabida dalilan kasuwanci, harda binciken cinikayyar da abokan ciniki, matakin tsaro, bincike/gyara, gudanar da ayyuka, binciken cikin gida din cigaba, da kuma inganci da lura da tsaro and tabbatarwa.

  3. RABAWA DA ABOKAN HUDDA NA WAJE
  4. Kundin dokar jama’a na Sashe 1798.83 ya bada dama ga abokan cinikayya wadanda mazauna California da su tambayi wasu bayanai game da bayyana bayanai zuwa ga abokan hudda na waje don yin tallen hajojin su. Bama raba bayanan abokan cinikayyar mu ga abokan hudda na waje da bamu tantance ba don yin amfani dashi wajen tallen hajojin su.

  5. MASU AMFANI KASA DA SHEKARA 18
  6. Kundin kasuwanci da ayyuka na California Sashe na 22581 yabaka damar, idan mazaunin California ne dan kasa da shekaru 18, ka kalla, gyara, ko kuma cire bayanai da ka bayar ko ka aika ga al’umma, ta hanyar shiga asusunka ko wani kaya ko aiki yadda ya kamata da gyara/cire bayanan ka. Kana bukatar lambobin sirri don shiga shafin ka. Kuma zaka tura mana sakon imel ko neman izinin cire wasu bayanai a rubuce ta hanyar amfani da adireshin mu dake fannin tuntubar mu na cikin wannan takarda.

    Cikin farin ciki zamu duba, gyara, ko kuma cire bayanai da/ko kuma abinda ya dace. Sauran diddigen bayanai da/ko kuma rubutu da aka cire daga asusunka da/ko kuma pejin mu zai iya zama a cikin wajen ajiyan mu ta ko-ta-kwana na kusan tsawon wata daya. Zamu iya rike bayanan ka don sulhunta rikici, tabbatar da bin yarjejeniya na mai amfani ko bin tabbatar da doka; a wannan hali, za’a tsare bayanan ka daga yin amfani dashi a wasu abubwan dabam.

  7. KADA KA BI SAITUKAN
  8. Kundin kasuwanci da ayyuka na California Sashe na 22575(b) ya bawa abokin ciniki mazaunin California sanin yadda muke mayar da martini ga nau’urar leka yana girzo akan saitin "Kada ka bibiya". Shi ka da ka bibiya sabon abu ne da akeyi, ba mu daukan wani matakai don martini ga saitin ka da ka bibiya, don haka muna bin dokar cikin wannan Manufar tsare Sirri. Idan kana neman karin bayani akan tsarin Ka Da Ayi Bibiya, zaka iya samu ta wannan hanyar shafin: http://www.allaboutdnt.com/.

  9. SAURAN HAKKOKI
    • Hakkin damar bayanan ka. Kana da hakkin na samun cikakkun bayanai akan ka da muka karba a watanni 12 idan ka nema.
    • Hakkin canjin sheka da bayanai. Kana da hakkin karbar bayanan ka ta hanyar iska a bisa yananyin da zaiyi amfani.
    • Hakkin sani. Kana da hakkin samun bayanai game da dalilan da yasa muka karbi bayanai akanka kuma muka raba, irin bayanan ka da muka siyar da kuma irin abokan hudda na waje da muka sayarwa da bayanan, sannan da irin bayanan ka da muka bayar sabida kasuwanci na tsawon watanni 12 idan ka nuna bukata.
    • Hakkin gogewa. Kana da hakkin ka nemi da mu goge bayanai akanka da muka karba daga wajenka. Zamu yi amfani da hayoyin fannin kasuwanci wajen jin koken ka, da bin dokokin da suka bada damar haka. Ka lura, cewa, zamu iya ajiye wannan bayanai, saboda dalilan halartaccen kasuwanci ko bin yadda doka ta tsara.
    • Hakkin fita daga tsarin. Kana da hakkin ka bamu umarnin daina bayyana bayanan ka da muke rabawa zuwa ga abokan hudda na waje don samun kudi ko wasu dalilan ta hanyar shiga shafin mu na "Ka Da A Sayarmin Da Bayanai Na".

  10. YADDA ZAKAYI AMFANI DA HAKKOKIN NAN
  11. Duk wani neman izini hakkokin mai amfani za’a iya aikawa zuwa mai shi ta hanyar lambar mu dake kasa. Wandannan neman izini za’a iya yinsu ne a kyauta kuma mai abun ne zaiyi da wuri kuma koda yaushe acikin wata daya. Duk wani neman izini, ayi kokarin rubuta cewa izinin yanada alaka da "Hakkokin Sirri na California" ka bayar da suna, adireshin ka, sunan gari, jahar ka, lambobin jaha, da kuma imel ko lambar waya da za’a iya tuntubar ka.

    Kafin mu yi martani ga neman da kayi, dokar California ta bamu damar tabbatar da kai dinne ta hanyar amfani da bayanan ka. Idan muka (ko muka nemi abokan hudda na waje don taimaka mana) sun kasa samar da abinda ka nema, zamu tuntubeka domin karin bayani. Idan muka kasa tabbatar da cewa kaine bayan gwadawa, zamu iya hanawa, sannan zamuyi maka bayanin dalilan hanawan.

    Zaka iya saka wakili ya tura nema, zai wakilce ka amatsayin ma’aikaci. Yadda zakayi, dole ka bamu a rubuce izinin da yaba shi ma’aikacin damar wakiltarka, kuma inda ya kamata, ya karbi bayanai akan ka. Kuma, kai da/ ko wakilin ka zaku bamu bayanai sosai da zai bamu damar tabbatar da cewa kaine.

  12.  BAYANAN TUNTUBA MU
  13. Bull City Learning, Inc.
    [email protected]