Taimako
Tambayoyin Da Aka fi Yi

Yi amfani da filin bincike da ke saman shafin domin binciko bidiyo ta amfani kebabbiyar kalma ko yankin jimla, kamar "shake test" ko "allurar rigakafi ta HPV." Ko ka zabi maudu'i daga jerin da ke karkashin "Yi bincike ta Maudu'i" akan shafin gida don ganin dukkan bidiyo a cikin kebabben rukuni.

Za ku iya kallo ko raba mahimman darussan bidiyo ba tare da amfani da data ta waya ko WiFi ba, amma ta amfani da siffar saukewa. Da farko, danna alamar a kan shafin video player ko daga kowane shafi inda bidiyon ta bayana. Idan ba ka shiga ta ciking asusunka ba, za a nemi ka shiga ta asusunka ko kirkiri wani.

Da zarar an sauke bidiyo, za ku iya kallo ta ko da ba ku kan intanet. Ku kulla cewa za sauke bidiyo ne kawai a lokacin da a ke da hadin WiFi ko intanet.

Bugu da kari, Manhajar Android ta Makarantar Rigakafi kan ba ku damar samun bidiyo da aka sauke bayan fita daga kan intanet daga na'urar Android.

Kara bidiyo cikin abubuwan da ku ka fi so domin ku sami sauƙin samunta da raba ta a nan gaba. Danna alamar daga video player ko daga kowane allo inda aka jera bidiyon. Duba cikakken jerin bidiyon da kuka fi so ta zabin “Bidiyo Na” daga jadawalin a hanun hagu saman allon ku.

Ku karkasa sannan ku raba bidiyonku zuwa rukuni-rukuni ta amfani da masarrafar jerin ababen kallo. Kara bidiyo a jerin ababen kallo ta zaben alamar tarawa daga bidiyo fileya daga kowane allo inda aka jera bidiyo. Kuna iya kara bidiyon ga jerin ababen kallo da ake da su ko ku kirkiri sabon jerin ababen kallo. Duba duk jerin ababen kallonku ta zaɓar “Bidiyo Na” daga babban jadawali a saman hagu na allonku.

Duka siffofin biyu kan bada damar samun bidiyo cikin sauki. Masarrafar ababen kallo kan ba ku damar rarrabe bidiyo ta ƙara su cikin jerin. Maida bidiyo wadda aka fi so hanya ce mai mataki dayada ke bada damar adana bidiyo cikin jerin da ba a rarrabe ba. Kara bidiyo cikin jerin ababen kallo ba ya adana bidiyon kai tsaye a cikin abubuwan da ka fi so. Sai dai kuma, bidiyo za ta iya kasancewa wadda ka fi so da kuma kasancewa cikin jerin ababen kallo.

Za ku iya bude take ta hanyar danna alamar take yayin da ku ke kallon bidiyo. Don rufe take, sake danna alamar.

Domin canza bidiyo ko take zuwa wani harshe daban, je zuwa jadawalin harsuna a can sama ka zabi harshen da ka fi so.

Tuntube mu.

Idan kuna da wata matsalar amfani da IA Watch wanda ba mu tabo ta ba a sama, ko aiko mana sakon imel da tamabayoyinku zuwa [email protected].