Za ku iya hada IA Watch cikin aikin ku a ta hanyoyi daban daban, da suka hada da:
Dukkan bidiyon suna bisa bayanin jagorar da WHO ta amince da shi kuma an kirkiro su ne da taimakon kwamitin bada shawarwari kan kiwon lafiya wanda ya kunshi kwararru na kasa da kasa da ma'aikata na cikin gida a fannin.
Dukkan bidiyon suna nan a Turanci, Faransanci da Swahili da Hausa, tare da sauran yaruka da za'a ƙara daɗewa.
A matsayin ɓangare na tsarin ƙirar ɗan adam, Reshen Cibiyar BCL ta gudanar da binciken sanin al'umma domin gano kalubalen da ake fuskanta yanzu da kuma fifita abubuwan da suka dace na masu sauraro da kuma masu ruwa da tsaki. Hirarraki masu zurfi, rukunonin tattaunawa, da zaman ayyuka.
An gudanar da su tare da rukunonin masu amfani a Tanzaniya. Bisa ga waɗannan bayanai da kuma a kan “ayyuka mafi kyau” na rigakafin kamar yadda WHO ta fasalta; an samar tare yarda da maudu'an bidiyo da aka ba fifiko tare da masu sauraro. Da zarar an yarda da shi, ana bincika kowane maudu'in bidiyo ta amfani da takardun jagora na WHO da kuma yin hirarraki tare da kwararru akan fannin.
Kwamitin kwararrun fanni ya yi bitar rubutattun bayanan bidiyo tare da sabunta su, haka kuma da masu ruwa da tsaki a Ma'aikatar Lafiya ta Tanzania. An gudanar da tsarin gyara da bita ba tare da katsalandan ba, ba tare da wasu alaƙa ba ban da waɗanda aka ambata a sama.
Waɗannan mutanen sun yi bitar duk takardun bayanai na horaswa sannan suka samar da jagora kan maudu'an horaswa na rigakafi.
Makarantar Rigakafi shiri ne na ilmantarwa na duniya wanda kwararu a fannin horaswa a Cibiyar BCL ke gudanarwa. Gidauniyar Bill da Melinda Gates ce ta ke daukar nauyin wannan yunkuri ta hanyar tallafin kudi kuma an kirkiro shi ta amfani da bayanin jagorar da WHO ta amince da shi, da ya hada da Horaswa ga Manajoji a Matakin Tsakiya (MLM) da rigakafi a aikace (IIP).