Manufar tsare Sirri

Bull City Learning, Inc.

Manufar tsare Sirri

Hakkoki da tonawa na wajen Amurka

Bull City Learning, Inc., tare da abokan harkokin su ("Bull City Learning", "mu", "mu", ko kuma "namu") ya dau alkawarin tsananta kare bayanan sirrinka, ko naka ko kuma a madadin mukarraban ka ("kai", "mai siya", ko kuma "mai amfani", ko kuma "naka").

Karin bayani akan hakkoki da aka bayyana a Manufar tsare Sirri yana aiki akan kowa, a wasu yanayin, mazauna wajen Amurka sun kasance sunada hakkoki bisa wasu bayanai da aka karba, amfani, da kuma rabawa bisa manufar tsare sirri.

Don wadannan dalilai, "Shafi" yana nufin shafuka, dandali, akwatunan sada zumunta, ko manhajar waya wanda za’a iya samun ayyukan koyo na Bull City a inda mai amfani zai iya ganin shafuka kuma yasamu izinin amfani da manhaja, kayayyaki, da ayyuka ("Aiki," gabaki daya "Ayyuka").

Don Allah ka samu lokaci ka karanta Manufar tsare Sirri na wajen Amurka sabida sirrin ka yanada muhimmanci awajen mu. Idan kanada wata tambaya akan yadda muke karbar bayanai, amfani, karewa ko yadda muke amfani da Bayanan ka (kamar yadda mukayi bayani a kasa), ka tuntube mu ta hanyoyin sadarwar mu dake kasa.

Saidai idan an canja yadda aka ayyana a wajen Amurka a wannan Manufar tsare Sirri, sharuda da akayi suna daidai da sharudan mu na amfani dashi. Idan kayi amfani da hajojin mu, ka amince da karba, ajiya, amfani da bayyana Bayanan kanka bisa yarjejeniyar da aka sanya.

  1. KARIN BAYANAI NA MASU AMFANI DAGA TARAYYAR TURAI
  2. Muna amfani da Bayanan ka ne a inda muke da doka ta bamu damar yin hakan. Muna amfani da Bayanan ka ne domin inganta Ayyukan mu, don bayar da ko taimaka wa hajar mu, ko kuma wani dalilin. Ya hada da, misali, amfani da Bayanan ka wajen bude maka asusu, gabatar da takarkari ko shiri da ka shiga; taimakawa wajen siyayyar da kayi, taimakawa wajen amfanin manhaja, bayar da kulawa ga abokan ciniki, ko tabbatar da jindadin masu amfani ta hanyar amfani da fasahar hana zamba kamar haramtawa ko kulle asusu.

    Zamu iya neman izinin ka wajen karba ko amfani da Bayanan ka sabida wasu dalilai. Wannan ya hada da, misali, samarda jaridar labarai, imel kai tsaye, da kuma tambayoyin ra’ayin ku akan kayayyakin mu da/ko Ayyukan mu da wasu hanyoyin talle.

    Muna amfani da dalilai bisa ka’ida wajen amfani da raba Bayanan ka. Wadannan dalilai harda: samar maka da taimako ga abokan ciniki ko gyara, bincike da inganta Ayyukan mu na yanzu da nan gaba, don baka kaya na musamman, jindadin amfani da ayyukan mu da kuma tuntubar ka bisa irin tallen da zai kayatar da kai, samar da hanyoyin cigaban Ayyukan mu, tabbatar da tsaro ga ayyukan mu da samarwa, jindadi da kariya akan wani matakin shari’a daga kowace kotu da takeda dama.

    Muna aiki da Bayanan ka bisa ka’idar da aka sanya mana kuma muke bi.

    Kana da damar hana mu amfani da Bayanan ka idan hakan yana iya zama matsala a yanayin da kake ciki. Zaka iya sarrafa yadda zamu dinga yi maka talla kuma kana da damar hana mu turo maka sakunan talla a kowanne lokaci idan kayi amfani da hanyar tuntuban mu a sama.

    A wasu yanayin, zaka iya neman muyi canjin wurin Bayanan da ka bamu. Zaka iya turo mana neman karin bayani kamar yadda yake a sashen tuntubar mu a kasa.

    Kamar yadda sai da yaddarka zamuyi amfani da Bayanan ka, kanada damar canja ra’ayin hanamu da Bayanan ka a kowanne lokaci.

  3. BAYANI GA MASU AMFANI MAZAUNA WAJEN AMURKA DA KUMA TARAYYAR CINIKAYYA NA TURAI (EEA)
  4. Idan bako ne kai a shafin ko sauran kayan mu da ayyukan mu na kan layi daga wajen Amurka, Bayanan da ka bayar, tsarawa da ajiyewa kai tsaye ko turawa zuwa wajen ajiyar bayanai a Amurka ko wasu kasashen da basu da dokokin kare bayanai kamar yadda yake a inda kake.

    Idan muka tura Bayanan ka na musamman zuwa wajen EEA muna yi ne bisa dokoki da aka yarda dasu a karkashin dokokin kare bayanai. Misali, idan muka tura Bayanan ka da aka karba a EU zuwa gurare awajen EEA, munayin haka ne bisa hanyoyin da Tarayyar Turai ta bayar don taimaka wajen bada tsaro, kamar Standard Contractual Clauses ko yardar shi mai Bayanan wajen turawa daga EEA zuwa kasar da ba EEA ba. Idan kayi amfani da Kayanmu, ka yarda da karba, turawa da kuma amfani da bayanan ka. Zamu iya tura bayanan ka na musamman don gabatar maka da Ayyukan mu bisa yarjejeniyar dake tsakanin mu.

  5. HAKKOKI MUSAMMAN NA EEA
  6. Idan kana zaune cikin kasashen Tarayyar Turai, idan ka nema, zamu baka duk wani bayanai akan ko mu rike wasu daga cikin bayanan ka tareda duk abinda doka tace a bayyana maka. A wasu lokutan, hakkinka ne akan:

    • gyara duka wani bayani akanka da ba daidai bane;
    • tare ko kayyade hanyoyin da muke amfani da Bayanan ka;
    • nuna rashin yarda da amfani da Bayanan ka;
    • ka nemi da a goge Bayanan ka, kuma
    • ka karbi shigen Bayananka a hanyar samun su cikin sauki.

    Ka tura saqon neman, ka tuntubemu a sashen tuntubarmu wanda ke kasa. Zamu mayar maka da martini cikin lokacin kadan.

    Haka kuma kana da damar janye yarjejeniyar yadda da amfani da Bayanan ka, idan dole amfani dasu din saida yardar ka. Zaka iya yin hakan ta daina yin amfani da Ayyukan mu, ta hanyar kulle duka asusunka na kan layi dake tare damu da kuma tuntubar mu a sashen tuntuba dake kasa tareda neman a goge Bayanan ka. Idan ka janye yarjejeniyar amfani da ko kuma raba bayanan ka sabida dalilan na cikin wannan Manufar tsare Sirri, bazaka iya amfani da duka(ko wasu) Ayyukan mu, kuma bazamu iya baka duka(ko wasu) daga cikin Ayyukan mu ba. Kuma kagane cewa, a wasu yanayin, zamu iya cigaba da amfani da Bayanan ka koda ka janye yarjejeniya kuma kasaka mu goge Bayananka, idan doka tabamu damar yin hakan. Misali, zamu iya rike wasu bayanai idan akwai bukatar yin hakan kuma bamu karya doka ba, ko kuma dole sai munyi hakan don kare Ayyukan mu bisa ka’ida.

    Idan kanada wani korafi akan ayyukan da muke gudanarwa bisa sirri, muna kira gareka da ka tuntubemu a sashen tuntuba dake kasa. Kuma kanada damar kai kuka zuwa hukumar kare bayanai na kasa (ana nufin hukuma masu lura da haka).

  7. BAYANAN TUNTUBA MU
  8. Bull City Learning, Inc.
    [email protected]