Manufar tsare Sirri

Bull City Learning, Inc.

Manufar tsare Sirri

Bull City Learning, Inc.,tare da abokan harkokin su ("Bull City Learning", "mu", "mu", ko kuma "namu") ya dau alkawarin tsananta kare bayanan sirrinka, ko naka ko kuma amadadin mukarraban ka ("kai"ko "mai siya").  

Manufar tsare Sirrin mu ("Manufar tsare Sirri" ko wannan "Yarjejeniya") anyi sa ne sabida a taimaka maka wajen fahimtar yadda muke karba, amfani da kiyaye bayanan da ka bamu da kuma taimaka maka wajen daukan matakin da yadace lokacin da kake amfani da kayan mu.   Domin sanin dalilan wannan yarjejeniya, "Shafi" rka duba shafukan mu, dandali, dandalin sada zumunta, ko wayoyin inda zaka iya samun ayyukan Bull City Learning wanda masu amfani dashi zasu iya shiga Shafi yanar gizo da shiga don amfani da manhaja, kayayyaki da/ko ayyuka (ko wanne "Aiki," da kuma gamin "Ayyuka").

Sirrinka yana da muhimmanci awajen mu. Sabida haka kasamu lokaci ka karanta wannan Manufar tsare Sirrin. Idan kanada wata tambaya akan yadda muke karbar bayanai, amfani, karewa ko yadda muke amfani da Bayanan ka (kamar yadda mukayi bayani a kasa), ka tuntube mu.

Saidai idan an canja yadda aka ayyana a wannan Manufar tsare Sirri, sharuda da akayi suna daidai da Ka’idojin Amfani kuma suna karkashin sharudodin da aka gabatar aciki. Idan kayi amfani da hajojin mu, ka amince da karba, ajiya, amfani da bayyana Bayanan kanka bisa yarjejeniyar da aka sanya.

I.               BAYANAN DA MUKE KARBA

Muna karbar "Bayanai akan kowa" da "Bayanan mutum."  Bayanai akan kowa wanda ya hada da bayanai da bazasu gane waye kai ba, kamar amfani da bayania a boye, bayani akan gari ko yanki zamu iya karba, shafukan aike/fita da adireshin yanar gizo, kalolin gurare, abubuwan da ka aika, abubuwan da aka samo ta dalilin bayanai da ka bayar da kuma yawan latsawa.  Bayanai akan mutum wanda ya hada da imel, lambar waya, adireshi, da sauran bayanai da katuro Shafi mu. Muna karban bayanai akan ka a dalilin gudanar da Ayyuka. Wadannan bayanai ya hada amma ba iyakan sunanka, wajen da kake zama, wajen aiki, adireshin imel da sauran bayanan samunka, kirgen yawan amfani da kakeyi da Ayyukan mu, da kalar harshe.

1.   Bayanai da aka karba ta hanyar fasaha. A kokarin inaganta Ayyukan mu, muna bibiyar bayanan da aka manhajar yanar gizon ka ko ta manhajar mu idan ka kalla ko kayi amfani da Ayyukan mu, harda Shafi da kashigo daga (wanda aka sani da "Shafi turowa"), kalar manhajar yanar gizo da kake amfani da, kalar na’urar da kake amfani, kwanan wata da lokacin da ka shiga, da sauran bayanai wadanda basu bayyana kai waye ba.  Muna bibiyar bayanai ta hanyar amfani da ma’ajiyar bayanai, ko karamar fayil din rubutu mai dauke da manuni na musamman.  Ana aika asusun bayanai zuwa manhajar yanar gizo daga kogin bayanan mu kuma ana ajiyesu ne acikin wajen ajiyar bayanai na na’ura mai kwakwalwar mai amfani dashi.  Tura asusun rike bayanai zuwa manhajar mai amfani da kayan mu yana bamu damar karbar bayanai akan mai amfani kuma zai ajiye tarihin abinda mai amfani yafiso yayinda yake amfani da Ayyukan mu, duka akan mutum daya ko wasu dayawa. Bull City Learning zaiyi amfani da duka asusun bayanai; na farko daga ciki zai zauna acikin na’ura mai kwakwalwar ka har sai ka goge su, na biyun kuma suna fita lokacin da ka kulle manhajar yanar gizon ka.   

2.   Bayanai da kabamu ta hanyar bude asusu. Bayan bayanan ka da muke samu kai tsaye daga manhajar yanar gizon ka duk lokacin da kashiga Shafi namu, don fara amfani da Ayyukan mu, kana da bukatan bude peji akan ka.  Zaka iya pejin ta hanyar yin rajista da Ayyukan ta shigar da suna, lambar waya, adireshin imel, da sauran bayanai naka da suna da kuma makullin sirri.  Idan kayi rajista, ka yarda kabamu damar amfani da karba, amfani da adireshin imel bisa wannan Manufar tsare Sirri. 

II.             YADDA MUKE AMFANI DA RABA BAYANAI 

Bayanai game da kai:

Saidai idan ba haka aka fadi ba a wannan Manufar tsare Sirri, bama siyar, ciniki, aro, ko kuma raba Bayanai game da kai bisa dalilan kasuwanci zuwa abokan hudda na waje ba tare da izininka ba. Muna raba Bayanai game da kai da abokan kasuwanci da sukeyin aiki ga Bull City Learning, sabida hadaka.  Wadannan abokan kasuwanci suna amfani da Bayanai game da kai bisa ka’idodin mu na Manufar tsare Sirri. Gabaki daya, Bayanai game da kai da kake bamu yana bamu damar taimaka wajen hudda da kai.  Misali, muna amfani da Bayanai game da kai wajen bada martani ga tambayoyi, neman tsokaci daga masu amfani dashi, taimako wajen gyara, da sanar da masu amfani dashi game da garabasoshi.

Zamu iya aika maka garabasoshi masu alaka ta Ayyukan mu wanda zaka iya fita idan bakaso ta cikin imel. Zamu iya aika maka bayanai masu muhimmanci game da asusun ka, amma bazaka iya fita ba. 

Bayanai ba game dakai ba:

 Gabaki daya, muna amfani da Bayanan don taimaka wajen inganta Ayyukan da saita yadda zakaji dadin amfani dashi.  Kuma muna rarraba Bayanai don samo abubuwan da ake yayi da kuma yadda zamuyi amfani dasu a Shafi namu.  Wannan Manufar tsare Sirrin bashida iyaka akan yadda muka amfani da Bayanai kuma munada damar yin amfani da tura Bayanan zuwa abokan hudda, masu tallace-tallace da wasu abokanan hudda na waje yadda mukeso. A inda kuma muka shiga wani cinikayya kamar gangami da wani kamfanin, ko wata kamfanin ta sayemu, ko siyar da wasu kadara ko duka, Bayanan ka zai iya kasancewa a tura harda su.  Ka yarda da amincewa zai iya faruwa kuma Manufar tsare Sirri yabamu damar turawa, kuma duk mai son siyan kadarar mu zai iya cigaba da duba Bayanan kamar yadda Manufar tsare Sirri yabada dama.  Idan yanayin da muke amfani da bayanai ya canja nan gaba, zamu fito da canjin da aka samu a manufar ga Shafi namu sabida ka fita daga sabon yanayin amfanin.  Muna baka shawara da kadinga duba Shafi lokaci zuwa lokaci idan kana da jaa akan yadda muke amfani da bayanai. 

III.          BAYANAI DA KE AKWAI TSAKANKANIN MASU AMFANI; TURA SAKONNI TSAKANIN MASU AMFANI

Yin amfani da Shafi yana bukatan yin rajistar asusu da bude peji inda zaka turo wasu bayanai naka wadanda suka hada da hoto, suna, wajen da kake (kasa), irin aikin da kake, yaren ka, da ayyukan asusu (wanda ya hada da yawan kallon bidiyo da kayi, wane kalar bidiyo ka kalla, lokutan da kayi amfani dashi wajen kallon, bidiyo da ka ajiye a gefe, bidiyo da ka nuna "kanaso", samun baje, da bidiyo da kuka kalla da wasu. Asali, wannan bayani an samar dashi ga wadanda sukayi rajista don sugani. Duk da haka, kana da zabin ka mayar da wasu daga cikin wannan bayanai naka kai kada sabida haka wasu masu amfani masu rajista baza su iya ganinsu ba. Zaka iya ganin bayanan da za a iya gani na sauran masu amfanin. Bayanan Shafi ka zai nuna ne kawai ga mutanen da sukayi rajista da Shafi; duk wanda yashigo Shafi kuma baaiyi rajista ba bazaiga bayanan ba.

Amfanin da zakayi da Shafi zaisa kuyi magana tsakanin ka da sauran masu amfani da Shafi ta hanyar tattaunawa a dandalin sakuna ko wata hanyar magana ta na’ura. Yawan sakunan da zaka dinga samu akai-akai, ko kuma rashin karbar sakon gabaki daya, zai alaka ne kalar ayyunkan da kake Ayyuka dashi da kuma yadda kake mu’amala da sauran masu amfani da Shafi.

Duk wani sadarwa tsakaninka da sauran masu amfani da Shafi yana karkashin Ka’idar Amfani da Binciken, kowanne yadda aka rubuta a Shafi mu Ka’idojin Aiki.Ka yarda da ka’idan mu a duka abubuwan,abinda aka kashe, da lalacewa ta hanyar rashin bin ka’idar dake nan. Idan ka zayyana wa wani bayanai game da kai ta hanyar sadarwa a cikin Shafi mu, to wannan kayi don kanka ne, sabida bazamu baka tabbacin cewa sirrin wannan bayanin zamu kareshi ba. Sabida haka, idan sadarwar ka da sauran masu amfani da Shafi yakai ga, amfani da hanyoyin sadarwa na waje wadanda basuda alaka da Shafi mu, ka yarda da cewa wannan sadarwar bashida kariyar Ka’idojin Aiki ko Manufar tsare Sirri. Kana yin wannan sadarwa a sane da hadarin da ke cikinta.

IV.             YADDA MUKE KARE BAYANAI

Muna amfani da hanyoyin tsaro wanda akayi su musamman don hana shiga batare da izini ba.  Asusunka yana samun kariyata hanyar lambobin sirri kuma muna baka shawara da ka rike bayanan ka ta hanyar boyesu da kuma fita daga asusunka duk lokacin da kagama amfani dashi.  Muna cigaba da kare bayanan ka daga matsalar rashin tsaro ta hanyar amfani da wasu hanyoyin fasaha harda boyewa, kariyar nau’ura da dai sauransu.  Duk da haka, wadannan matakan basuda garanti cewa baza’a iya samun bayanan ka ba, a fitar dashi canjawa ko rusawa da hanyar kaucewa tsaron da aka saka akai.  Idan kayi amfani Ayyukan mu, ka yarda kuma ka amince da hatsarin fitar wadannan bayanai. 

V.           HAKKINKA GAME DA AMFANI DA BAYANAI AKANKA

Kanada damar akowanne lokaci ka hanamu tuntubar ka akan tallace-tallacen mu.  Idan muka tura sakon talla ga mai amfani ds Shafi mu, zai iya fita daga irin wadannan sakunan ta bin haryar fita daga irin sakunan ta imel. Kuma a lura cewa ko da kafita daga karbar irin sakonnin tallace-tallace ta saitin Shafi, zamu cigaba da turo maka sakonnin imel na ayyukan mu wanda suka hada da, misali, sabunta Manufar tsare Sirri akai-akai, da sauran bayanai. 

VI.             BAYANAN ABOKIN CINIKI 

"Bayanan abokin ciniki" yana nufin duka wani bayani da akayi amfani ko ajiyewa akan Aikin abokin ciniki ko a madadin sa, da kuma duk wani bayani da aka samo daga wajen. Bayanan abokin ciniki harda, babu iayaka: (1) bayanin da aka bayar akan Aikin;(2) bayanin da masu amfani ko abokan hudda na waje suka baiwa Bull City Learning; da kuma (3) bayanai da aka gane game da abokan ciniki, masu amfani da Shafi, ko wasu abokan hudda na waje. 

(a)  Shiga, Amfani, & Dolen Shari’a. Saidai idan an samu rubutacciyar amincewa, Bull City Learning:

  • bazasu shiga, aiki da, ko kuma amfani da bayanan abokin ciniki idan ba wanda yazama dole ba sabida gudanar da Ayyukan;
  • bazasu bama ma’aikatansu damar shiga bayanan abokin ciniki ba saidai a inda ma’aikacin yazama masa dole sai yashiga bisa rubutacciyar yarjejeniyar rashin tonawa da Bull City Learning kare wannan bayanin, kamar yadda yake a wannan sashen; kuma
  • bazai ba abokan hudda na waje bayanai na abokin ciniki ba. Duk da haka, Bull City Learning zasu bayar da bayanin abokin ciniki idan doka ta bata wannan damar ko kuma gwabnati idan ta nemi hakan. Bull City Learning zasu sanar da abokin ciniki idan akwai bukatar gwabnati ko kotu da kuma hadin kan abokin cinikin wajen ganin an cimma buri ko kuma zasu ki amincewa da hakan a madadin abokin cinikin. 


(b)  Hakkokin abokin ciniki. Saidai idan ba’a saka a wannan yarjejeniyar ba, abokin ciniki yanada kuma ya rike duka hakki na bayanan sa, kuma Bull City Learning suna amfani da rike wannan bayanan ne a madadin abokin cinikin.

VII.             HANYOYI ZUWA WASU SHAFUKAN

Daga cikin irin Ayyukan, zamu iya baka hanyoyin ko wanda sukayi daidai da wasu shafukan ko wayoyi.  Duk da haka, bamu da hakkin tsarin sirri, bayanai ko kaya da wadannan shafukan suka kunsa.  Wannan Manufar tsare Sirrin yana aiki ne akan bayanan da muka karba game da Aiki ta Shafi nan.  Sabida haka, wannan Manufar tsare Sirrin bai kasance akan amfani da Shafi abokan hudda na waje da ake shiga ta hanyar su a Ayyukan mu ba.  Har zuwa shiga ko amfani da Ayyukan ta wani Shafi ko waya, yanayin tsarin manufar sirrin wannan Shafi ne zaiyi amfani akan shigar da kayi.  Muna bama masu amfani da kayanmu shawarar su karanta bayani akan sirri wasu shafukan kafin su shiga suyi amfani dasu. 

VIII.           CANJIN DA MUKAYI GAME DA MANUFAR TSARE SIRRI

Bull City Learning nada damar canja wannan manufa da kuma ka’idojin amfani a ko wanne lokaci.  Zamu sanar da kai idan ansamu canji gameda Manufar tsare Sirri namu ta hanyar turo maka sako a adireshin ka na imel ko kuma mu saka acikin Shafi mu.  Canji masu muhimmanci da aka samu zai fara aiki bayan kwana 30 da bada sanarwar.  Canji marasa muhimmanci zasu fara aiki ne a lokacin. Ka dinga duba Shafi akai-akai da kuma Shafi sirrin don ganin sabon abubuwa. 

IX.       HAKKOKIN SIRRI NA CALIFORNIA

Idan mazaunin California ne kai, kanada karin hakkin sirri. Don cikakken tattaunawa akan wannan hakkin, duba Hakkoki da Tonawa na California.

X.             ABOKAN CINIKI KO MASU AMFANI DASHI NA WAJEN AMURKA

Idan kai mazaunin wajen amurka ne, ka duba Hakkokin Tarayyar Turai da Sauran inda ba Amurka ba.

XI.             TUNTUBE MU

Idan kanada tambaya akan wannan Manufar tsare Sirrin ko ayyukan Shafi nan, ka tuntubemu ta hanyar tura mana sakon imel zuwa [email protected].

An sabunta wannan Manufar tsare Sirrin Ranar 23, 2020.