Horaswar Bidiyo Kyauta ga Kwararru a aikin Rigakafi

Kalli gajerun darussan bidiyo kan muhimman maudu'an rigakafi, da suka hada da kayan samar da sanyi, isar da allurar rigakafi, lula da bayanai, da karin wasu.

Yadda Kwararru a aikin Rigakafi 60,000+ suke Amfani da IA Watch:
Sami Amsoshi Duk Lokacin Da Ku Ke Bukatarsu.

Ko kuna lissafin adadin hasara ko hada kaya zuwa aikin rigakafi, IA Watch kan samar da darussa bisa bukata da za a iya saukewa don amfani ba akan intanet ba.

Koyi Sabon Ilimi Kuma Ka Bunkasa takardun Cancantarka

Duk lokacin da ka kalli bidiyo ka koyi sabon ilimi, ka sami daraja da matsayi a shafin yanar-gizo. Kowane matsayi na tagulla, azurfa, zinari ko farin karfe a cikin kowane maudu'i akan shafin yanar-gizo.

Inganta Kwazon Kungiyarku

Raba darussa nan da nan da wasu ta WhatsApp ko imel. Yi amfani da bidiyo lokacin tallafawar kulawa ko lokacin bada horon kan aiki. Dukan darussa na samuwa cikin Turanci, Farasanci, Hausa da Swahili.

Yi rijista da IA Watch don samun duk wadanan muhimman abubuwa da wasu.
Yi rijista yanzu