Mun fadada damar kai wa kadara mafi girma ta IA Watch: al'ummarmu ta dubban kwararru masu aikin rigakafi.
Yanzu, za ku iya yin tambayoyi, ku haɗu tare da takwarorinku ta hanyar ma'ajiyar adireshin membobi, kuma ku ga yadda wasu ke haɓaka iliminsu na rigakafi ta hanyar allunan maki da jeri ababen kallo na jama'a.
Ga yadda za ku iya amfani da sabbin siffofin cudanyar akan IA Watch don haduwa tare da sauran masu rajista da ke amfani da ita.
Kuna iya duba furofayil na daidaiku a cikin Ma'ajiyar sunayen, wanda ke sauƙaƙe samu da haɗi tare da takwarorinku. Kuna iya lalubo furofayil na membobin al'umma, ku ware ta suna ko ƙasa, ko ku binciko abokan aiki a cikin kebabbun ayyukan yi, ta amfani da mataci.
Kuna iya ganin jerin bidiyo da wasu membobi suka kirkira don koyon kansu, da kuma waɗanne bidiyo ne suka kalla, suka fifita ko suka rarraba ga wasu. Nemi masu amfani da ke da irin wannan sha'awar ko koya daga jerin ababen kallo na bidiyo da suka kirkira.
Mun yi hadin gwiwa tare da masana rigakafi don samar da kumshen jerin ababen kallo, wadanda za a ambata a fadin shafin yanar-gizo. Kowane jerin ababen kallo na ƙwararru zai nuna bidiyo da aka zaɓa wadanda wani fitaccen masani a duniya ya tabbatar da amfani da kuma dacewarsa. Za ku iya ƙarin koyo game da masana ta hanyar duba bayanan furofayil din su.
Don bayyana cigaban yawancin membobin al'umma da ake aiki tare, muna ƙaddamar da allunan maki kan shafuka maudu'i. Allunan maki za su nuna matsayi ga manyan masu koyo cikin kowane maudu'i, da aka yi wa matsayi a tsarin nasarori. Daukaka matsayinka a cikin kowane rukuni ta hanyar kallon bidiyo, wanda zai taimaka maka samun matsayi akan allon maki a tsakanin takwarorinka da suka fi cin nasara.
Hadu tare da al'ummar IA Watch ta siffar aika sakonni mafi sabunta. Yi tambayoyin da suka dace kuma rarraba amsoshin a kan allunan sako na shafin maudu'i, wadanda ke samuwa ga dukkan masu amfani da ke da rijista.
Idan dama kana da asusu, muna ƙarfafa maka guiwa don ka kammala furofayil din ka ta ƙara hoto, masayin aiki, da ƙasar ka. Idan ba ka taɓa yin rijistar asusu ba, saita ɗaya yanzu don farawa. Dukkan furofayil na IA Watch za su bayyana ga sauran masu amfani da ke da rijista. Idan kuna son kula da furofayil na kebe, ko iyakance abin da sauran masu amfani ke iya gani, za ku iya samun damar saitunanku na kebe ta shafin furofayil din ku.
Kirƙiri asusunka yau don samun damar sababbin siffofin IA Watch kuma ka haɗa tare da rukunin kwararun rigakafinmu na duniya.
Yi rijista yanzu