Kaddara cewa wata uwa ta kawo yaro zuwa cibiyar kiwon lafiya da ka ke aiki. An yi wa yaron allurar rigakafi kwana daya da ya wuce kuma yanzu yana fama da kumburi a wurin da aka yi allurar. Da zarar ka duba yaron, yana da muhimmanci ka kawo rahoton al'amarin.