Game da Mu

IA Watch, bangaren Makarantar rigakafi, shafin yanar-gizo ne da ke da gajerun fayafayan bidiyo domin saurin koyon ilimin rigakafi daga kan waya ko laptop din ku.
IA Watch kan ba ka dama ka:
  • Kalli bidiyo a kan intanet ko bayan ka sauka
  • Bibiyi aikin koyon ku da ci gaba
  • Kirkiri jerin abubuwan da ka fi so ko bidiyon da aka fi kallo
  • Sami kwararen daraja da takadun shaida

Za ku iya hada IA Watch cikin aikin ku a ta hanyoyi daban daban, da suka hada da:

  • Don ingantawa da wartsake iliminku
  • A matsayin abin la'akari na gani yayin da a ke yin mahimman ayyuka
  • Don taimakawa cikin sadarwa tare da sauran membobi ma'aikata
  • Don ƙarfafa duba aiki na tallafawa
Amintacen Kunshi

Dukkan bidiyon suna bisa bayanin jagorar da WHO ta amince da shi kuma an kirkiro su ne da taimakon kwamitin bada shawarwari kan kiwon lafiya wanda ya kunshi kwararru na kasa da kasa da ma'aikata na cikin gida a fannin.

Dukkan bidiyon suna nan a Turanci, Faransanci da Swahili da Hausa, tare da sauran yaruka da za'a ƙara daɗewa.

Tsarin Edita

A matsayin ɓangare na tsarin ƙirar ɗan adam, Reshen Cibiyar BCL ta gudanar da binciken sanin al'umma domin gano kalubalen da ake fuskanta yanzu da kuma fifita abubuwan da suka dace na masu sauraro da kuma masu ruwa da tsaki. Hirarraki masu zurfi, rukunonin tattaunawa, da zaman ayyuka.

An gudanar da su tare da rukunonin masu amfani a Tanzaniya. Bisa ga waɗannan bayanai da kuma a kan “ayyuka mafi kyau” na rigakafin kamar yadda WHO ta fasalta; an samar tare yarda da maudu'an bidiyo da aka ba fifiko tare da masu sauraro. Da zarar an yarda da shi, ana bincika kowane maudu'in bidiyo ta amfani da takardun jagora na WHO da kuma yin hirarraki tare da kwararru akan fannin.

Kwamitin kwararrun fanni ya yi bitar rubutattun bayanan bidiyo tare da sabunta su, haka kuma da masu ruwa da tsaki a Ma'aikatar Lafiya ta Tanzania. An gudanar da tsarin gyara da bita ba tare da katsalandan ba, ba tare da wasu alaƙa ba ban da waɗanda aka ambata a sama.

Kwamitin Bada Shawara

Waɗannan mutanen sun yi bitar duk takardun bayanai na horaswa sannan suka samar da jagora kan maudu'an horaswa na rigakafi.

  • Dakta. Francois Gasse, UNICEF
  • Dakta. Renu Paruthi, Ofishin Kasa na WHO a India
  • Bonaventura Nestory, Ma'aikatar Lafiya ta Tanzania
  • Dakta. Jean-Marc Olive, memba na WHO IPAC (Kwamitin Bada Shawara na Aikin Rigakafi), ya yi ritaya daga WHO
  • Dakta. Frida Mghamba, Ma'aikatar Lafiya ta Tanzania Dakta. (a da)
  • David Brown, Kamfanin Brown Consulting Group
  • Dakta. Alex Mphuru, Ma'aikatar Lafiya ta Tanzania (a da)
  • Dakta. Robin J. Biellik, PATH (ya yi ritaya) da WHO (ya yi ritaya)
Masu Daukar Nauyinmu

Makarantar Rigakafi shiri ne na ilmantarwa na duniya wanda kwararu a fannin horaswa a Cibiyar BCL ke gudanarwa. Gidauniyar Bill da Melinda Gates ce ta ke daukar nauyin wannan yunkuri ta hanyar tallafin kudi kuma an kirkiro shi ta amfani da bayanin jagorar da WHO ta amince da shi, da ya hada da Horaswa ga Manajoji a Matakin Tsakiya (MLM) da rigakafi a aikace (IIP).